✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai mutum 9,000 masu cutar COVID-19 a Najeriya

NCDC ta ja hankalin jama'a kan muhimmancin matakan kariyar COVID-19.

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC, ta ce adadin mutanen da ke dauke da cutar COVID-19 ya kai 9,066 bayan samun karin mutum 565 da suka kamu a ranar Juma’a.

NCDC ta bayyana hakan ne a shafinta na Intanet da safiyar ranar Asabar.

  1. Yajin aikin likitoci ‘shirme’ ne —Ngige
  2. Kishi ya sa wata mata cinna wa kanta wuta a Jigawa

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa an samu karin sabbin mutum 9,033, wadanda aka dauki bayanansu

NCDC ta bayyana cewa mutane 76 sun warke kuma an sallame su daga cibiyoyin killace masu cutar daban-daban da ke kasar a ranar Juma’a.

Hukumar Kula da Lafiyar Jama’a, ta ce ya zuwa yanzu adadin wadanda suka warke ya kai 165,409 a cikin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).

Alkaluman NCDC sun nuna an samu sabbin wanda suka kamu daga jihohi 16 na Najeriya a ranar Juma’a.

Dangane da sabbin bayanan NCDC, Legas ce ke da mafi yawan adadin masu kamuwa da cutar da mutum 348, sai Ribas  mai mutum 70 da kuma mutum 45 Akwa Ibom.

Sauran sun hada da Oyo (36), Abuja (24), Ekiti (15), Kwara (7), Ogun (7), Gombe (3) sai Anambra da Kaduna da mutum biyu kowannensu.

Jihohin Beyalsa, Kuros Riba, Edo, Filato, Kano da Sakkwato na da daya kowane.

Hukumar ta bayyana cewa adadin wanda cutar ta harba sun kai 177,142, yayin da mutum 2,178 suka mutu a jihohi 36 da Abuja.