✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yuwuwar cutar Shan-inna ta sake dawowa Najeriya – UNICEF

UNICEF ta ce har yanzu nasarar da aka samu a bangaren rigakafin ba ta taka kara ta karya ba.

Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya ce akwai yuwuwar cutar Shan-inna ta sake dawowa Najeriya.

Jami’ar Tsare-tsaren ci Gaba ta asusun, Elizabeth Onitolo wacce ta bayyana hakan ta lura cewa barazanar ta sake tunkarowa ne shekaru biyu bayan Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ba kasar shaidar fatattakar cutar gaba daya.

Tana jawabi ne a yayin wata tattaunawa a kan rigakafin cututtuka da ta annobar Corona da hukumar ta UNICEF ta shirya a Yola, jihar Adamawa ranar Litinin.

An shirya tattaunawar ne da gudunmawar Sashen Kare Hakkin Yara na Ma’aikatar Watsa Labarai ta Jihar.

Onitolo ta ce har yanzu nasarar da aka samu a bangaren rigakafin ba ta taka kara ta karya ba.

Ta ce har yanzu iyaye da dama ba sa ba da hadin kai kuma har yanzu babu isassun jami’an lafiya da na tsafta wadatattu a yankuna da dama.

“Hanya daya tilo da za mu iya magance faruwar hakan ita ce ta tabbatar da cewa kowanne yaro ya sami cikakkiyar kulawa da kuma kariya. Bai kamata cutar da za a iya maganceta ta sake kashe wani yaro ba. Sekaru biyu kenan ba a sami cutar ba a Najeriya, kuma ba ma so ta sake dawowa,” inji jami’ar.