✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Almajirai sun daina bara a Kebbi

Na tsani ganin almajiraina suna cin sauran abinci, inji alaramma.

Bisa dukkan alamu tsarin makarantun allo ya dauki sabon salo a Jihar Kebbi, kasancewar almajirai sun daina yin barar abinci kamar yadda aka saba.

Aminiya ta gano cewa yawancin alarammomin makarantun na ba wa almajiransu kwarin gwiwa su rika ribatar lokacin da ba na makaranta ba su koyi sana’o’i domin dogaro da kansu.

Sabanin yadda aka saba ganin almajirai na yawon barar abinci, ko da kuwa suna yin ’yan kananan sana’o’i, abin ya sauya yanzu, inda alarammomi ke yawan jaddada wa daliban nasu muhimmancin yin sana’a.

A da can manyan almajirai kadai ne malaman ke bari su je su koyi sana’a, amma yanzu har yara ’yan shekara 10 zuwa 12 daga cikinsu sun fara koyo ko yin sana’o’i.

Wani almajiri mai shekara 11, ya shaida wa Aminiya cewa malaminsa ne ya sa koyi sana’ar gyaran takalma tun shekara uku da suka wuce.

Yaron ya ce yakan je ya yi sana’ar ce a tsakanin lokacin karatun safe da na yamma da kuma ranakun hutu, inda yake samun N200 zuwa N400 a kullum.

Shi ma wani almajiri mai shekara 10, ya shaida wa Aminiya cewa ya koyi sana’ar gyaran farce ne shekara biyu da suka wuce.

Sai dai ya ce karancin shekarunsa ya sa mutane ba su cika ba shi aiki ba, saboda ya nemi wata sana’ar.

Ya ce a halin yanzu ya fara koyan aikin wankin mota garin Birnin Kebbi, kuma yana samun abin da ke iya rike shi.

Almajirin ya shaida wa wakilinmu cewa yakan samun har N3,000 a wurin wankin motar a ranakun da babu makarnata, domin a ranakun yakan yi aiki ne tun daga safiya har zuwa lokacin tashi.

Daya daga cikin alarammomin da Aminiya ta samu zantawa da su, Alaramma Muhammadu, ya ce yana karfafar almajiransa su koyi sana’a.

Ya ce daga cikin abin da ya sa yake hakan shi ne ya tsani ganin almajiransa suna barace-barace ko cin ragowar abincin wasu.