✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliya: Ganduje ya ba da umarnin fara rushe-rushe a Kantin Kwari

Hakan ya biyo bayan samun ambaliya a kasuwar

Biyo bayan ambaliyar ruwan da aka samu a Kasuwar Kantin Kwari da ke Kano, Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da umarnin fara rusa duk wani gini da aka yi a kan hanyar ruwa a cikin kasuwar.

Umarnin zai kuma shafi kwatar Kwarin Gogau da ke cikin birnin na Kano.

Sauran wuraren da za a rusa sune ilahirin gine-ginen da aka yi a kan kwalbatocin da ke kewaye da kasuwar don a ba ruwan sama da shara damar wucewa ba tare da wata matsala ba.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya sanar da hakan, lokacin da yake yi wa ’yan jaridar Fadar Gwamnatin Kano jawabi kan batutuwan da Majalisar Zartarwar jihar ta tattauna ranar Laraba.

Bayan karbar rahoton irin barnar da ambaliyar ta yi a kasuwar wanda Kwamishinan Ayyuka, Injiniya Idris Wasa Saleh da na Muhalli, Kabiru Ibrahim Getso suka gabatar, Majalisar ta kuma ba da umarnin cire dukkan tebura da rumfunan wucin gadin da aka kafa a kan magudanun ruwan da ke kewayen kasuwar ba tare da bata lokaci ba.

Idan za a iya tunawa, kasuwar ta fuskanci mummunar ambaliya a cikin makon nan, wacce ta jawo ’yan kasuwar suka ce sun tafka asarar daruruwan miliyoyin Nairori.