✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Ruwa: Aisha Buhari ta raba tallafin N10m a Binuwai

An raba tallafin a tsakanin mutane 200 da ambaliyar ruwan ta shafa.

Uwargidan Shugaban Kasa, Aisha Buhari, ta bayar da tallafin naira miliyan 10 domin rage radadin mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa a Jihar Binuwai.

Aminiya ta ruwaito cewa, Aisha Buhari ta ba da tallafin ne ta hannun mai dakin dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu.

Bayanai sun ce Aisha Buhari ta ce a raba tallafin a tsakanin mutane 200 da ambaliyar ruwa ta janyowa asarar muhallai da dukiya a Makurdi, babban birnin jihar.

Tuni dai Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (SEMA) a Binuwai, ta ce an raba tallafin ga wadanda ibtila’in ambaliyar ya rutsa da su.

Babban Sakataren SEMA, Dokta Emmanuel Shior ya ce sun raba kudin ne ga kauyuka biyar da abin ya fi shafa a Makurdin.