✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ambaliyar ruwa ta datse hanyar Bauchi zuwa Gombe

Mamakon ruwa sama ya sanya masu ababen hawa cikin tasku.

Ambaliyar ruwa ta datse babbar hanyar Bauchi zuwa Gombe, lamarin da ya bar masu ababen hawa suka yi curko-curko.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura reshen jihar Bauchi, Yusuf Abdullahi, ya ce daya daga cikin manyan kwalbatin da ruwa ke bi ta datse sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a kwanakin nan.

Aminiya ta ruwaito cewa, wannan shi ne karo na biyu cikin kasa mako uku da ambaliyar ruwa ke hana matafiya wucewa ta hanyar.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, ya ce a yanzu matafiyan da suka taso daga Adamawa zuwa Abuja, sai dai su bi hanyar Gombe zuwa Dukku Darazo zuwa Bauchi da kuma Jos zuwa Abuja.

A halin yanzu an tura jami’an tsaro kan hanyar don tabbatar da kubutar ababen hawa, da kuma kiyaye salwantar rayuka ko dukiyoyin al’umma.