✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a Taraba

Ambaliyar dai ta biyo bayan ruwan da aka sha kwarya ranar Asabar.

Sama da gidaje da wuraren kasuwanci 200 ne ambaliyar ruwa ta shafe a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba, bayan wani ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama ana tafkawa ranar Asabar.

Ambaliyar dai ta biyo bayan ruwan da aka sha kamar da bakin kwarya wanda ya fara tun misalin karfe biyu na dare har zuwa wayewar gari.

Yawancin wuraren da ambaliyar ta shafa masu makwabtaka da kogin Mayo Gwoi ne da mahadar Magami a garin na Jalingo.

Rahotanni sun ce lamarin ya yi sanadiyyar shanyewar gadar Mayo Gwoi, wanda tilas ya sa masu amfani da ita suka yi curko-curko.

Kazalika, bincike ya nuna kayan abinci da dabbobi da sauran kayan amfanin yau da kullum na miliyoyin Nairori ne suka salwanta sanadiyyar ambaliyar.

Wani mazaunin daya daga cikin yankunan da lamarin ya shafa, Malam Musa Dauda ya ce gidansa da na makwabtansa duk sun nitse a ruwa, ta yadda dole sai da suka yi kaura domin tsira da rayuwarsu.

A wani labarin kuma, Shugaban Karamar Hukumar Jalingo, Nasiru Bobboji ya yi kira da a samar da kayan agajin gaggawa da magunguna ga wadanda ambaliyar ta shafa a Jihar.

Tuni dai aka rufe gadar ta Mayo Gwoi domin hana ababen hawa bi saboda alamun tsagewa da aka gani a jikinta sanadiyyar ambaliyar.