✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ambaliyar Ruwa: Tinubu ya ba Kanawa tallafin N100m

Tinubu ya yaba wa Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a Jihar Kano.

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da tallafin Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Kano.

Tinubu, wanda ya kai ziyarar kwanaki biyu birnin na Dabo, ya bayar da tallafin ne yayin wata liyafar dare da kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano ta shirya domin karrama shi.

Ya ce ya bayar da tallafin ne a yunkurinsa na taimakawa waje rage radadin ambaliyar ruwa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Aminiya ta ruwaito Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta jihar ta bayyana cewa, an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 19 cikin 44 na jihar, inda mutane 23 suka mutu, 106 suka jikkata, sannan gidaje 12,919 sun rushe yayin da gonaki 14, 496 suka lalace a kananan hukumomi biyar daga ciki.

Da yake jawabi a wurin liyafar, Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa bambance-bambancen Najeriya ya zama tushen samar wa kasa arziki idan ya zama zababben shugaban kasa a 2023.

Tinubu ya yi alkawarin sake dora masana’antun kasar a kan turbar gogayya da takwarorinsu na duniya ba kawai ga Arewa ko Kano ba har ma da kasa baki daya.

Ya kuma yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar, inda ya bayyana gwamnan a matsayin “aboki kuma amintaccen abokin tarayya.”

Ya kuma yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.