✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Amfanin ’yancin kai ga talakan Najeriya

Shekara 61 da samun mulkin kai amma Najeriya na kwan-gaba-kwan-baya

Shekara 61 ke nan da samun ’yancin kan Najeriya daga Turawan mulkin mallaka.

Kuma tun daga ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960 da Turawan Ingila suka mika ragamar mulkin kasar nan ga shugabannin gwamnatin hadaka a karkashin jagorancin Firai Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa, ’yan kasa ke shirya bukukuwa don raya wannan rana.

Sukan bayyana farin cikinsu da jin dadi da samun ’yanci da damar tafiyar da dukkan harkokin da suka shafi al’ummar Najeriya, ba tare da neman amincewar Sarauniya ko Razdan ba.

Turawan mulkin mallaka sun shafe tsawon shekaru suna bautar da ’yan Afrika, suna kwashe musu albarkatun kasa suna gina kasashensu, suna sarrafa kudaden haraji da tattalin arziki yadda suka ga dama bisa umarnin Sarauniya.

Kuma su ne ke tsara wa jama’a yadda za su rayu ko tafiyar da harkokinsu na rayuwa, a wani bangaren ma hatta addini da al’ada sai da suka tsara yadda za a gudanar da su.

Sai dai duk da irin satar dukiyar kasa da turawa suka rika yi, suna samar da ingantattun hanyoyin mota da na jiragen kasa, ko da kuwa domin samun saukin fitar da albarkatun kasar da suka sace ne zuwa masana’antun kasashensu.

Sun kuma samar da makarantu da asibitoci masu inganci, wadanda wasunsu har yanzu ana cin moriyarsu, wasu kuma an yi musu kwaskwarima ana ci gaba da amfana da su.

’Yan Najeriya da dama a lokacin suna da ayyukan da suka dogara da su, wadanda suka shafi kasuwanci, da kwadago, sai noma da kiwo, wadanda suka rike iyalai da matasa wajen inganta rayuwarsu.

Kowa ya dade…

A lokacin duk wanda aka samu yana zaman kashe wando to shi ya ga dama, saboda akwai dama iri-iri da mutum zai jingina da su.

Idan abin mutum ya waiwayi abubuwan da suka faru a wancan lokacin ne, kafin karbar ’yancin kai, duk da kasancewar wasunmu ba su ma zo duniyar ba, amma tarihi ya tabbatar da yadda Turawan mulkin mallaka suka bar kasar nan da abubuwan cigaba da suka samar, domin ’yan kasa wadanda suka karbi mulki su dora daga inda suka tsaya. mutum zai yi takaicin yadda ake samun koma-baya da lalacewar al’amura, wadanda ake dora alhakinsu kan rashin samun shugabanci nagari, da rashin kishin kasa daga gare mu.

Duk da kasancewar an samu damar da za a ninka irin cigaban da aka gada daga hannun Turawa sakamakon gano arzikin man fetur da ya yi sanadiyyar kawo wa kasar kudade masu yawa, wancan zargin da aka yi a baya, na rashin shugabanci nagari da rashin kishin kasa, ya sa aka rika al’mubazzarantar da dukiyar da take shigowa, aka rika yi wa dokokin kasa hawan kawara.

Abin da ke raba kai

Siyasar kabilanci da bangaranci ta ci gaba da haifar da rabuwar kai a tsakanin ’yan Najeriya, aka watsar da harkokin gona, aka koma rayuwar kura tsira da na bakin ki, abin da ya dada jefa kasar cikin wani yanayi na daga-ba-gidana-ba-sai-gidan-’ya’yana.

Aka sauya salon tafiyar da tsarin shugabanci daga salon mulki irin na Ingila mai Firai Minista da Shugaban Gwamnati, zuwa tsarin siyasar kasar Amurka mai shugaba guda daya tilo mai cikakken iko.

Wadannan da wasu dalilai da ba zai yiwu na kawo su duka a nan ba, ko saboda karancin ilimi da shekaru, ko saboda gudun rubutun ya gunduri mai karatu, sun taka rawa wajen haifar da kiki-kakar da kasar ta samu kanta a ciki.

Amma ko shakka babu, duk wani dattijo da ke da wayo kan abubuwan da suka kasance a baya, ya dubi yadda rayuwar kasar nan take a halin yanzu, zai bayyana maka takaici da yadda kasar take dada samun kanta.

Ko da yake ba za a nuna yatsa ga wani mutum ko bangare da za a dora wa alhakin lalacewar kasar nan ba, saboda yadda al’amura suka rika warwarewa a hankali, har suka kawo halin da muke ciki na yanzu,amma a duk rana irin wannan, a kan samu wasu ’yan kasa da ke ganin babu wani abin yiwa biki, don kuwa ’yan kasa ba su ci moriyar ’yancin da aka samu ba.

Jiya i yau

Tattalin arzikin Najeriya na ci gaba da kwan gaba kwan baya, yau a ce an samu bunkasa da nasara, wadanda akasari a rubuce ne ba a zahirin rayuwar ’yan kasa ba, gobe kuma a sake yin warwas, da kwance uwa kwance.

Talauci na ci gaba da galabaitar da ’yan Najeriya, yayin da rashin aikin yi a tsakanin matasa ke dada jefa kasar cikin kalubalen tsaro.

Shi ya sa idan kana hira da dattijai za ka ji ana tuna maka da karin maganar nan ta Bahaushe da ke cewa, kowa ya tuna bara bai ji dadin bana ba.

Ko da yake kuma ba adalci ba ne a rika auna bara da bana, musamman a yanayin zamantakewa ta Najeriya, saboda sauyin zamani da bunkasar da kasar ta yi.

An samu karuwar al’umma daga kimanin mutane miliyan 46 a lokacin samun ’yancin kai a 1960, zuwa mutane fiye da miliyan 200.

An samu karuwar marasa aikin yi, da yawaitar yaran da ke yawo a titi babu karatu, da karuwar kungiyoyin ’yan bindiga, masu ta da kayar baya da masu satar dukiya da mutane, don neman kudin fansa.

Duk da kasancewar Najeriya giwar Afrika, daya daga cikin manyan kasashen duniya masu karfin soji da damar fada a ji a Majalisar Dinkin Duniya, kasar na da kwararrun likitoci, da ma’aikatan lafiya da sauran kwararru da a ko wacce rana suke neman hanyar fita waje, saboda samun kyakkyawar kulawa a wasu kasashen duniya, a yayin da harkokin lafiya da ilimi ke kara tabarbarewa, duk kuwa da kokarin da gwamnatoci ke cewa suna yi wajen daidaita al’amura.

Ma’aikata na ganin tasku

Rayuwar ma’aikacin gwamnati ta tashi daga abin sha’awa zuwa abin takaici, saboda rashin ingancin albashi da kyautatuwar yanayin aiki, inda har wasu ma ke gwammacewa su yi kasuwanci da kwadago don ciyar da iyalinsu, a maimakon jiran albashin da bai wuce cikin cokali ba, wanda da kyar yake yi wa karamin ma’aikaci mako guda.

Ba na goyon bayan masu ra’ayin cewa bai kamata a yi wata murna don samun ’yancin kai ba, ina ganin ko babu komai abin farin ciki ne, kasancewar mu ne muke mulkar kan mu.

Kuma har yanzu Najeriya ta ci gaba da zama dunkulalliyar kasa, duk kuwa da yunkurin da wasu suke yi na ballewa ko kafa kasar kansu, domin tunanin za su fi kafa tsarin da zai samar musu da cigaba.

Tsarin dimukradiyya da kasar nan ta samu kanta a ciki ya kara kusantar da talakawa kusa da gwamnati, jama’a da dama sun amfana da mulkin siyasa.

Wasu tsare tsare da gwamnati ke kirkirowa lokaci zuwa lokaci suna bai wa wasu ’yan Najeriya damar cin moriyar wani abu daga arzikin kasa.

Musamman a karkashin gwamnati mai ci, tsare-tsaren yaki da talauci da aka bullo da su sun taimaka wa mutane da dama samun madogara da inganta sana’o’insu na neman abinci.

A lokacin da a wani bangaren kuma ake zargin ’yan siyasa da raba kan ’yan kasa, haddasa matsalolin tsaro, da satar dukiyar kasa, da kuma karya tattalin arziki, lamarin da ya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin wani mawuyacin hali.

Kowa ya mike

Lallai ne, a maimakon mu ci gaba da kokawa da bayyana takaici, da la’antar shugabanni, mu rika amfani da wannan lokaci wajen duba hanyoyin da za mu gyara gaba, ta hanyar amfani da duk wata dama da ’yancin kai ya ba mu, mu mutunta junanmu a matsayinmu na ’yan Najeriya, kuma mu mutunta kasarmu a matsayinta na uwa, kuma gatanmu a duniya, wadda in babu ita, babu wata kasa da za ta karbe mu a matsayin ’ya’yanta, sai dai mu yi ta galantoyi a matsayin ’yan gudun Hijira.

Firai Ministan Najeriya na farko, kuma wanda daga kansa babu wani, Sa Abubakar Tafawa Balewa, cikin jawabinsa na samun ’yancin kai, ya yi kira ga ’yan Najeriya mu yi amfani da wannan dama mu ga mun tafiyar da al’amarin kasarmu da kyau.

Ko wanne dan Najeriya, komai matsayinsa ko bangarensa, ko wanne addini yake bi, ya ba da gudunmawa ga cigaban kasar nan.

Wannan shi ne muhimmin sakon da har yanzu ake isarwa ga ’yan Najeriya.

Idan ba mu sanya kishin kasa da kishin al’ummarmu ba, son zuciya da mugunta ne za su hallaka mu kuma su ci gaba da lalata kasar mu.

Ina kira ga ’yan uwana matasa, a maimakon dauke dauken hotuna da sanya tufafi masu launin tutar Najeriya ana dorawa a zaurukan sada zumunta, ya kamata mu yi amfani da lokacin wajen tunatar da kawunan mu nauyin da ke kanmu na nuna kishin kasa da jajircewa, don ganin Najeriya ta samu sauyi mai ma’ana da zai kawo cigaba mai dorewa, a duk wata dama da suka samu, a maimakon neman damar da su ma za su wawuri arzikin kasa su kudance lokaci daya, su da iyalansu.

Allah Ya kawo mana sauyi a Najeriya da cigaba mai ma’ana wanda kowa zai amfana da shi a matsayinmu na ’yan kasa.

Abba Abubakar Yakubu, ya rubuto wannan sharhi ne daga Jos