Amurka na zawarcin hulda ta gaskiya da nahiyar Afirka —Blinken | Aminiya

Amurka na zawarcin hulda ta gaskiya da nahiyar Afirka —Blinken

Blinken yayin da yake jawabi a Jami’ar Pretoria
Blinken yayin da yake jawabi a Jami’ar Pretoria
    Ishaq Isma’il Musa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken da ke ziyara a Afirka ta Kudu, ya ce Amurka na zawarcin hulda ta gaskiya da nahiyar Afirka, sannan kuma ba ta gasa da wata babbar kasa a duniya wajen neman karbuwa a nahiyar ta Afirka.

Tun a Lahadin da ta gabata ce, Mista Blinken ya isa Afrika ta Kudu domin fara ran-gadin kasashen Afirka uku wanda ke zuwa jim kadan da kammala ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov ya kai nahiyar.

A yayin gabatar da jawabi ga taron manema labarai a babban birnin Pretoria na kasar Afrika ta Kudu, Sakataren Harkokin Wajen na Amurka ya ce, ba sa kallon nahiyar Afirka a matsayin wani fagen gogayya da manyan kasashen duniya.

A wannan ran-gadin da ya soma a nahiyar Afirka, Mista Blinken ya fara yada zango ne a Afirka ta Kudu, kasar da ke zama jagora a jerin kasashen duniya maso tasowa wadda kuma ta dauki matsayin ’yan ba-ruwanmu a rikicin Rasha da Ukraine.

Afrika ta Kudu dai ta yi kememe, inda ta ki bin sahun kasashen Yammacin Duniya wajen sukar gwamnatin Moscow da ke kaddamar da farmaki a Ukraine.

Mista Blinken din ya kuma sanar da wasu sabbin manufofin Amurka a nahiyar Afirka a wani jawabi da ya yi a jami’ar Pretoria.