✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta cire Sudan daga jerin kasashe masu taimaka wa ta’addanci

Ofishin jakadancin Amurka ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

Amurka ta cire kasar Sudan daga jerin kasashen masu taimaka wa ayyukan ta’addanci, shekara 27 bayan sanya sunan Sudan din a cikin jerin kasashe masu taimaka wa ’yan ta’adda.

Ofishin Jakadancin Amurkar a Khartoum, hedikwatar Sudan, ya ce Sakataren Harkokin Wajen Kasarsa ya sanya hannu a takardar cire Sudan daga cikin masu taimaka wa ta’addanci a duniya.

Sanarwar ta ce umarnin wanke Sudan daga zargi zai fara aiki ne daga Litinin 14 ga Disamba, 2020.

A watan Oktoba, Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta cire Sudan daga jerin kasashen da ake zargi da taimaka wa ayyukan ta’addanci.

Sai dai a lokacin sabuwar gwamnatin ta ki amincewa da tayin saboda wasu bukatu da Amurka ta gabatar mata a kan hakan, duk da cewa hare-hare na hana masu zuba jari daga waje shiga kasarta.

Daga baya ta amince da biyan diyyar Dala miliyan 335 ga wadanda suka sha da kyar, da iyalan wadanda hare-haren da aka kai Ofisoshin Jakadancin Amurka a Kenya da Tanzania a  shekarar 1998 suka hallaka.

Gwamnatin wucin gadin Sudan, wacce ta dare madafun iko bayan kifar da gwamnatin tsohon Shugaba Omar al-Bashir a 2019, ta kuma amince da Isra’ila a matsayin kasa mai zaman kanta.