✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amurka ta miƙa wa MDD daftarin tsagaita wuta a Gaza

Wannan ne karo na 6 da Blinken ke kai ziyara Gabas ta Tsakiya tun bayan faro luguden wutar Isra’ila.

Amurka ta gabatar da wani daftarin kudiri ga kwamitin sulhu na MDD wanda ya bukaci a tsagaita wuta a Gaza tare da sako ragowar mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken ya sanar da hakan ne a yayin wata hira da ya yi da Kamfanin Dillacin Labaran Kasar Saudiyya na Al Hadath.

A cewar babban jami’in diflomasiyyar Amurkan, yana fatan kasashe mambobin kwamitin za su mara baya ga wannan daftari domin samar da mafita ga rikicin na Gaza da ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula.

Mista Blinken dai na rangadi ne a yankin Gabas ta Tsakiya a kokarin warware rikicin Isra’ila da kungiyar Hamas wanda ya shiga wata na shida, inda ya fara daga Saudiyya kuma zai yada zango a wannan Alhamis a kasar Masar kafin daga bisani ya isa birnin Doha na kasar Qatar.

Tun a cikin daren jiya Laraba, Mista Blinken ya isa Saudiyya don tattaunawa da mahukuntan kasar da ke matsayin jagora tsakanin kasashen Larabawa a kokarin kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin da Isra’ila ke ci gaba da yi a yankin Gaza.

Blinken wanda wannan ne karo na 6 da ya ke kai ziyara Gabas ta Tsakiya tun bayan faro luguden wutar Isra’ilan kan al’ummar yankin Gaza, da zuwa yanzu ya hallaka kusan mutum dubu 32 tare da raba wasu miliyan 1 da dubu 500 da muhallansu.

Bayanai sun ce bayan kammala tattaunawa a Saudiyya, zai kuma yada zango a Masar inda zai tattaunawa da wasu jagororin yankin na Falasdinu a birnin Alqahira.

Mista Blinken dai ya samu tarba daga Yarima Faisal bin Farhan, sakataren wajen Saudiyan a Riyadh yayin da kowanne lokaci daga yanzu ake tsammanin Blinken ya samu ganawa da Yarima mai jiran gado na Saudiyar, Muhammad bin Salman.

A yayin tattaunawar, Yarima Faisal bin Farhan ya jaddada wa Sakataren Amurka bukatar da ke akwai na ganin Isra’ila ta kare rayukan fararen hula.

Ziyarar ta Blinken na zuwa ne a wani yanayi da yunwa ke ci gaba da kisan tarin kananan yara a yankin na Gaza ciki har da sabbin haihuwa a daidai lokacin da al’ummar Musulmi ke azumin watan Ramadana.

Haka kuma, lamarin na zuwa ne yayin da a bangare guda Isra’ila ke zafafa hare-hare hatta a kan masallata, inda cikin kasa da sa’o’i 24 ta hallaka mutane fiye da 100 daga jiya zuwa yau.

Duk da cewa batun samar da yarjejeniyar tsagaita wuta ya fi daukar hankali a tattaunawar amma wasu majiyoyi sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa yayin zaman na yau Alhamis, shugabannin na Larabawa za su gabatar wa Amurka wani kunshin kudiri da suke ganin zai kawo karshen rikicin na tsawon shekaru tsakanin Isra’ila da Falasdinu.