✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An cafke masu satar mutane biyu bayan kashe yaran da suka yi garkuwa da su

Jami’an rundunar ’yan sanda a Jihar Osun sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da ta’adar satar mutane bayan sun kashe wadansu yara da…

Jami’an rundunar ’yan sanda a Jihar Osun sun cafke wasu mutane biyu da ake zargi da ta’adar satar mutane bayan sun kashe wadansu yara da suka yi garkuwa da su.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Olawade Olokode ne ya tabbatar da hakan ranar Juma’a a hedikwatar ’yan sanda da ke Osogbo, babban birnin Jihar.

CP Olokode ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 28 ga watan Janairun 2021 a kan hanyar Durojaye da ke yankin Iludum  na Jihar.

Kwamishinan ’yan sandan ya ce ababen zargin sun amsa laifinsu na garkuwa da kuma kashe kananan yaran biyu da suka tsare.

Ya ce an tsinto gawar yaran a wani jeji da ke yankin Oka-Bale inda ababen zargin suka yasar da su.

Kazalika, ya ce za a gurfanar da su a gaban Kuliya da zarar sun kammala binciken da suke gudanarwa.