✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tsare shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Gwamnati ta gurfanar da Kanu a gaban kotu ranar Talata bayan ta cafke shi.

Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin tsare Shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, a hannun hukumar tsaro ta DSS.

Bayan cafke Kanu, jami’an DSS sun gabatar da shi a gaban Mai Shari’a Binta Nyako ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a ranar Talata.

A lokacin zaman ne kotun ta ba da umarnin DSS ta ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da za kammala shari’ar, bisa bukatar lauyan Antoni Janar na Tarayya, Shuaibu Labaran, domin a baya Kanu ya tsere bayan kotu ta bayar da belinsa.

Mai Shari’a Binta Nyako ta kuma dage sauraren shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Yuli, 2021.

Da misalin karfe 1:40 na ranar Talata aka gabatar da Kanu, a kotun cikin tsauraran matakan tsaro, a yayin da jami’an tsaro suka hana shiga harabar kotun a lokacin zaman.

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da damke Nnamdi Kanu, wanda ya dade ana neman sa ruwa a jallo bisa zargin cin amanar kasa da kuma ayyukan haramtacciyar kungiyar ta IPOB.

Tuni dai Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya tabbatar da cafke Nnamdi Kanu, wanda Gwamnatin Tarayya ta riga ta ayyana kungiyarsa ta IPOB a matsayin ’yar ta’adda.

Wani hoto da ke yawo a kafafen sadar da zumunta ya nuna Nnamdi Kanu a hannun jami’an tsaro, an sa masa ankwa a hannuwansa.

Kungiyar ta dade tana kalubalantar kasancewar Najeriya a matsayin kasa daya dunkulalliya, kuma take ci gaba da yin fito-na-fito da hukumomin kasar.

A baya-bayan nan, IPOB ta yawaita kai hare-hare a kan hukumomi da gine-ginen gwamanti.

Maharan kungiyar sun kashe jami’an tsaro da dama, baya ga kona ofisoshin ’yan sanda a yankin Kudu maso Gabas.

Baya ga haka, a ranar 12 ga watan Yuni —Ranar Dimokuradiyya—  kungiyar ta tilasta wa mutanen yankin zama a gida, saboda zargin yiwuwar tayar da rikici ko kai hare-hare.

Wasu daga cikin manyan shugabannin yankin, ciki har da ’yan siyasa sun nesanta kansu da ayyukan kungiyar.

Kasa da mako biyu ke nan da kungiyar ta kulla kawance da ’yan tawayen kasar Kamaru.