✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An cafke ’yan canji 6 kan sace dan abokin sana’arsu

Su yi garkuwa da dan abokin sana'arsu mai shekara takwas

Wasu ’yan canji su shida sun shiga hannun hukuma kan zargin satar dan wani abokin sana’arsu.

Ana zargin ’yan cajin sun hada baki sun sace karamin yaron mai shekara takwas a duniya ne a Jihar Legas.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya ce, “Sai bayan kwana uku aka sako yaron a cikin wani bahu da hannunsa da kafafunsa a daure.”

Hundeyin ya bayyana ta shafinsa na Twitter cewa duk wadanda ake zargin abokan sana’ar mahaifin yaron da aka sace ne, kuma a wuri daya suke harka tare da shi a Legas.

Ya ce rundunarsu tana ci gaba gudanar da bincike kan lamarin.

(NAN).