✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kamfanin jiragen sama ya fara zirga-zirga daga Abuja zuwa Jigawa

Jirgin ya fara tashi ne da fasinjoji 20 ranar Litinin

Kamfanin sufurin jiragen sama na Overland, a ranar Litinin ya fara zirga-zirga daga Dutse, babban birnin jihar Jigawa, zuwa Babban Birnin Tarayya Abuja.

Jirgin kamfanin samfurin 5N-BM dai ya fara jigilar ce da fasinjoji akalla 20 a cikin jirginsa mai cin fasinjoji 50.

Manajan Darakta kuma Shugaban kamfanin na Overland, Kyaftin Bayo, ya ce kamfanin zai tsaya da kafarsa a jihar.

Da yake jawabi ga ’yan jarida a Dutse, shugaban ya ce Gwamnatin Jihar ta rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar fahimta tsakaninta da kamfanin mai zaman kansa ta fara zirga-zirgar daga Dutse zuwa Abuja.

Shi ma Gwamnan Jihar, Muhammad Badaru Abubakar ya tabbatar da hakan a filin jirgin saman na kasa da kasa da ke Dutse, yayin zantawarsa da Aminiya.

Gwamnan, wanda Mataimakinsa, Malam Umar Namadi ya wakilta, ya ce kasancewar Allah Ya albarkace su da noma da kiwo, jihar na da abubuwa da dama da za ta fitar zuwa ragowar sassan Najeriya da ma kasashen waje.

Ya kuma ce, “Hakan zai inganta kasuwanci a jiharmu, kuma muhimman abubuwa da dama za su zo jihar, sannan shi ma kamfanin na Overland zai samu amfani mai yawa.”

Namadi ya kuma yi alkawarin cewa Gwamnatin Jihar za ta mutunta dukkan alkawuran da ta dauka daga bangarenta a yarjejeniyarta da kamfanin don ganin zirga-zirgar ta dore.