✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto matafiya 13 daga hannun masu garkuwa

’Yan sanda da mafarauta sun ceto matafiya 13 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Jami’an ’yan sanda da mafarauta sun kubutar da wasu matafiya 13 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su.

A ranar Asabar aka kubutar da mutanen da aka sace su ranar Alhamis daga maboyar ’yan bindigar da ke hanyar Ahor a kan babbar hanyar Benin zuwa Auchi a Jihar Edo.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Edo, Philip Ogbadu, ya ce an yi amfani da jirage marasa matuka da kuma mafarauta da ’yan banga wajen ganowa da ceto mutanen daga dajin da aka kai su cikin nasara.

Ya bayaya cewa an yi garkuwa da matafiyan ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa Legas daga Akwa Ibom da Onitsa.

Ya ce an kai wadanda aka ceto din asibiti domin tabbatar da lafiyarsu kafin a mika su ga gwamnati domin su karasa zuwa garuruwansu.

Ya kara da cewa an gano maboyar masu garkuwa da mutane guda bakwai a cikin dazukan a yayin kokarin gano inda aka yi a matafiyan da aka sace.

A don haka, Ogbadu ya roki mazauna yankin da su rika taimaka wa jami’an tsaro da bayanan motsin masu garkuwa da mutane, tunda a wurin mutane bata-garin ke zuwa sayen cefane.