✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daddatsa fasto a Kogi, an jefa gawarsa a kwata

An tsinci gawar ne a cikin wata kwata da ke dab da cocin Faston

An tsinci gawar wani Faston majami’an Deeper Life da ke Karamar Hukumar Okehi ta jihar Kogi, bayan an daddatsa shi, sannan aka jefa gawarsa a cikin kwata.

Marigayin dai an ce yana kan hanyarsa ce ta koma wa gida bayan kammala ibada a coci a garin Okaito da ke kan hanyar Kabba zuwa Okene a jihar ta Kogi, lokacin da aka hallaka shi.

Aminiya ta gano cewa kisan nasa ba ya rasa nasaba da wani raba tallafi da ake zarginsa da yin sama da fadi da shi.

Ana dai zargin masu raba tallafin ne da karkatar da shi ba tare da raba wa wadanda ya kamata ba.

Tuni dai aka kama mutum uku da ake zargi da hannu a kisan wanda aka yi ranar 10 ga watan Maris, 2022.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar ta Kogi, SP Williams Aya, ya shaida wa Aminiya cewa an tsinci gawar Faston ce a wata kwata da ke kusa da cocinsa, kwanaki kadan bayan an nemi shi an rasa.

Ya ce tuni rundunar ta cafke mutum uku bayan samun wasu bayanan sirri, inda ya ce yanzu haka suna Sashen Binciken Manyan Laifuffuka inda ake fadada bincike a kan su.

Sai dai SP Aya ya ce rundunar ba za ta bayyana sunan wadanda ta kama din ba, saboda tana ci gaba da farautar ragowar.