✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da ‘yan Majalisa na wata tara a Kaduna

Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna ta dakatar da tsohon Mataimakin Shugabanta Mukhtar Isa-Hazo na wata tara saboda da wasu ‘ya’yanta guda biyu bisa zargin yunkurin…

Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna ta dakatar da tsohon Mataimakin Shugabanta Mukhtar Isa-Hazo na wata tara saboda da wasu ‘ya’yanta guda biyu bisa zargin yunkurin tsige shugabanta.

Sauran mutum biyn da aka dakatar su ne Nuhu Goroh-Shadalafiya mai wakilar Kagarko da kuma Yusuf Liman-Dahiru mai wakiltar mazabar Kakuri/Makera.

Zaman da Mataimakin Shugaban Majalisar Isaac Auta-Zankai ya jagoranta ya kuma umarci wasu ‘yan majalisar biyar su nemi afuwa su kuma wallafa a jarida cikin mako guda.

Matakin ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin binciken da majalisar ta kafa kan yunkuri hambarar da shugabancinta a ranar 11 ga watan Yuni.

Kwamitin da Shehu Yunusa mai wakiltar Kubau ya bayar da shawarar daukar matakin a kan wadanda abun ya shafa kamar yadda dokar majalisar ta yi tanadi.

Ana zargin su da haifar da rabuwar kai da rikicin tsakanin ‘yan Majalisar da cin mutuncin shugaban majalisar.

Wadanda za su nemi afuwar su ne tsohon shugaban majalisar Aminu Abudllahi Shagali, mai wakiltar Sabon Gari da kuma Salisu Magajin Gari.

Sauran su ne Abdulwahab Idris, Ikara; Yusuf Salihu, Kawo; da kuma Nasiru Usman, Tudun Wada.