✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsige shugabannin majalisa da na kananan hukumomi 4 a Jigawa

Ana zargin shugabannnin kananan hukumomin da badakala, ’yan majalisar kuma shirin tsige shugabansu

An tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mai Tsawatarwa na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.

Majalisar ta kuma dakatar da shugabannin kananan hukummi hudu, bayan karbar rahoton kwamitocin da ta kafa.

An tsige jagororin majalisar ne bayan samun su da laifin kitsawa da kuma goyon bayan yunkurin tsige shugaban majalisar a makonnnin da suka gabata.

Dan majalisa mai wakiltar Malam Madori, Hamza Ibrahim Adamu, ne ya gabatar da kudurin, wanda ya samu amincewar takwarorinsa.

Nan take bayan tsige Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Aliyu Ahmed, mai wakiltar Kirikasamma da kuma Mai Tsawatarwa, Dayyabu Shehu Kwalo, mai wakiltar Taura, majalisar ta maye gurbinsu.

Mambobin majalisar sun kuma dakatar da shugabannin kaknanan hukumomin Auyo, Dutse, Gumel, da Ringim, kan zargin badakalar kudade.

Rahoton shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar, Aminu Zakaria Tsibut, ya shida wa zauren mata cewa kwamitinsa ya gano badakalar kudade a yayin aikinsa na sa ido a kananan hukumomi 27 na jihar.

Majalisar ta ce dakatar da shugabannin kananan hukumomin alama ce ta shirinta na bin diddigin kudade da kuma yin komai a fili a matakin gwamnatin jiha da kananan hukumomi.