✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakile yunkurin sace daliban sakandare a Kaduna

Sojoji sun dakile yunkurin ’yan bindiga na sace daliban makarantar sakandare.

Sojoji sun dakile sabon yunkurin ’yan bindiga na yin garkuwa da daliban makarantar sakandare a Jihar Kaduna ranar Juma’a.

An fatattaki maharan ne sa’o’i kadan bayan ’yan bindiga sun kashe wani dalibi, suka harbi wani, tare da yin garkuwa da malamai biyu da dalibai da dama a Kwalejin Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya a Jihar.

Jami’an tsaron sun tarwatsa bata-garin da suka kai hari makarantar  sakandaren Prelude Comprehensive College da ke Kujama a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar ne bayan samun bayanan sirri.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce bayan samun rahoton ne sojoji da ’yan sanda suka yi gaggawar isa makarantar suka dakile harin.

Ya ce hakan ya sa maharan kaucewa, suka sauya hanya suka tsere ta hanyar Kaduna zuwa Kachia.

“A nan suka tare hanya suka yi awon gaba da mutum biyu, amma jami’an tsaro sun kwato su bayan sun bi masu garkuwar.

“Amma maharan sun harbi wasu mutum uku, wadanda aka kai asibitin St. Gerard da ke Kaduna ana jinyar su.”

Rahotanni daga Jihar ta Kaduna sun kuma nuna jami’an tsaro sun bindige wani dan fashi da ke sanye da kayan sojoji a Makarfi, da ke kan babbar hanyar Zariya zuwa Kano, aka kuma kwace wata bindiga daga hannunsa.