An daura auren budurwa mai shekara 55 a duniya | Aminiya

An daura auren budurwa mai shekara 55 a duniya

Budurwar mai shekara 55 da saurayinta mai shekara 62
Budurwar mai shekara 55 da saurayinta mai shekara 62
    Abdullahi Abubakar Umar

Wasu rahotanni sun bayyana cewa an daura auren wata budurwa mai shekara 55 da saurayinta mai 62 a Jihar Osun da ke Kudancin Najeriya.

Budurwar mai suna Esther Bamiloye da saurayinta Isaac Bakare ’yan asalin Jihar Osun, sun kulla igiyar aure ta farko a tahirin rayuwarsu kamar yadda Jaridar Punch ta wallafa.

Esther ta ce tun bayan da ta isa aure take zuba ido ko wani zai zo neman aurenta amma lamarin ya ci tura sai a yanzu da ta kai shekara 55 sannan kaddara ta riga fata.

Ta bayyana cewa a duk tsawon shekarun da ta yi a duniya bata taba soyayya da kowa ba har sai da Allah Ya kawo mata wannan saurayi da a yanzu ya zama mijin nata.

Kafin wannan lokaci, Esther ta ce ta shiga damuwa sosai na rashin auren amma daga baya abin ya daina damunta.

Kazalika, ta ce ta yi iyaka bakin kokarinta na kare budurcinta kasancewar duk jiran da ta yi tana neman mijin auren bata taba sanin wani da namiji ba sai bayan da ta yi aure.

Esther ta yi godiya ga Allah da Ya cika mata burinta da ta dade tana fata a rayuwarta.