✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana binciken masu satar bayanan sirri su yada a kafafen sada zumunta

Majalisa ta nuna damuwa ka yaduwar bayanan sirri a kafafen sa da zumunta.

Majalisar Tarayya ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike a kan yadda ake satar bayanan sirri daga hukumomin tsaro, wanda hakan ke kawo cikas ga yunkurin samar da tsaro a sassan Najeriya.

Majalisar Wakilai ta umarci kwamitinta na Tsaro da Tara Bayanan Sirri ya gudanar da binciken ne ganin yadda ake yawan satar muhimman bayanan  tsaro daga hukumomin ana yadawa a kafafen sada zumunta da sauran kafafe.

Da yake gabatar da bukatar binciken a zauren majalisar, Honorabul Samuel Babatunde Adejare ya bayyana damuwa kan yadda bayanan sirri kan tsaron kasa suke yawo a kafafen sa da zumunta da na jaridu da dangoginsu.

A cewarsa, “Hakan yana gurgunta duk wani yunkuri na yaki da ’yan bindiga da ’yan ta’adda da sauran manyan laifuka a Najeriya.”

“Idan aka bar wannan matsala ta ci gaba ba tare da an magance ta ba, to za a wayi gari tana barazana ga rayukan jami’an tsaro da ma kasar nan baki daya.”

Ya bayyana cewa yoyon bayanan sirrin na taka muhimmiyar rawa wajen haifar da koma baya da ake samu a bangaren tara bayanan sirri, da kuma rashin fahimta da rabuwar kai tsakanin hukumomin tsaro a wajen yaki da masu aikata manyan laifuka.

Adejare ya ce abin takaici ne “yadda hakan ke taimaka wa masu aikata wasu nau’ikan manyan laifi kamar fasa gidajen yari da garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda da satar shanu da amfanin gona.”

Bayan ya gabatar da kudurin cikin nuna damuwa ne Majalisar ta ba wa kwamitinta na tsaro mako biyu ya mika mata rahotonsa.