✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fitar da sunayen wadanda suka yi nasarar samun NDA

Za su hallara a NDA ranar 6 ga Afrilu, 2021 domin fara samu horo

An fitar da sunayen wadanda suka samu gurbin zama hafsan soji cikin wata shida a Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin Soji ta Najeriya (NDA) karo na 47.

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta sanar da haka a safiyar Juma’a, tana mai shawartar wadanda suka nemi gurbin zaman hafsan soji cikin wata shida su duba sunayensu a shafinta.

Latsa nan don ganin sunayen wandan suka yi nasara.

Rundunar ta umarce su da cewa, “Wajibi ne wadanda suka yi nasara su hallara a harabar tsohuwar NDA da ke Kaduna daga ranar Talata 6 ga Afrilu, 2021.

“Wadanda ba su hallara ba zuwa karfe 6 na yammancin ranar Laraba, 7 ga Afrilu, 2021, sun rasa ke nan, za a maye gurbinsu da wadanda sunayensu ke jerin masu jiran ko-ta-kwana,” inji Rundunar.

Sanarwar dauke da sa hannun Sakataren Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya, Manjo Janar GAT Ochigbano ta ce ana bukatar sabbin kananan hafsoshin su je da abubuwa kamar haka:

a. Ainihin takardun shaidar karatu da kuma kwafin shaidar rajistar neman gurbin na SSC 47 na intanet mai dauke da hotonsu

b. Hotuna kala masu girman 5×7 da aka dauka a tsaye babu hula

c. Fararen riguna kanana guda hudu marasa rubutu ko kwala da gajerun wanduna ruwan shanshambali (marasa layi)

d. Bakaken wanduna dogaye guda biyu

e. Takalman kambas kafa biyu (banda takalman roba ba)

f. Fararen mayafai biyu da rigunan filo

g. Bargo daya (fatsi-fatsi ko ruwan kakin soja)

h. Seti daya na kayan cin abinci

i. Kayan zaman gida kala biyu

j. Jam’ian soji daga cikinsu za su zo da takardar shaidar sakin su da kuma hutu daga kwamandojinsu.

Allah Ya sa a dace.