✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama likitan bogi kan zargin kashe mai juna biyu a Kano

Mai juna biyu ta yi gamo da ajalinta ne a kokarin zubar mata da cikin shege da ta dauka.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani likitan bogi kan zargin yi wa wata mai juna biyu allurar zubar da ciki, lamarin da ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Tun da farko wani mai suna Nura Balarabe da ke zaune a Kwanar Mahuwa ta Karamar Hukumar Tofa da ke Jihar Kanon ne ya yi karar wani Ukasha Muhammed, wanda mazaunin garin Langel ne a Karamar Hukumar Tofa.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, Nura Balarabe ya yi karar Ukasha Muhammad ne kan zargin yi wa kanwarsa mai suna Amina Bala ciki.

A cewarsa, Ukasha Muhammad ya hada baki da wani likitan bogin mai suna Chidera Ugwu mazauniyar garin Lanbum Banki a Karamar Hukumar Tofa, inda ya yi mata allura tare da ba ta wasu magunguna da niyyar zubar mata da cikin da ta dauka, lamarin da ya yi sanadiyyar ajalinta.

Kakakin Rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa jami’ansu sun kama dukkanin wadanda ake zargin kuma duk cikinsu babu wanda ya musanta laifin da ake zargin sa da shi.

Kiyawa ya bayyana cewa, mafarar bincike da suka yi ya nuna ana zargin cewa Chidera Ugwu ya dade yana yi wa masu juna biyu a garin allura da ba su magunguna, lamarin da ke janyo musu matsaloli da dama.

Kiyawa ya kara da cewa Kwamishinan ’yan sandan jihar CP Usaini Gumel ya bayar da umarnin fadada bincike tare da gurfanar da wadanda ake zargin gaban kuliya don girbar abin da suka shuka.