✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama magidanci kan kashe matarsa a Adamawa

Magidanci mai shekaru 40 ya yi wa matarsa kisan gilla a Jihar Adamawa.

’Yan sanda sun kama wani magidanci bisa zargin yi wa matarsa kisan gilla a Jihar Adamawa.

Rundunar ’yan sandan jihar ya ce  mutumin dan shekara 40 dan asalin garin Bode da ke karamar hukumar Shelleng na jihar  ne.

Ana zargin bayan ya kashe matar mai suna Godiya Akwale, sannan ya kulle gawarta a cikin gidansu kafin ya tsere zuwa Jihar Ondo.

Ma’auratan sun yi aure sama da shekara uku.

Kakakin ’yan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya tabbatar wa Aminiya kama wanda ake zargin.

Ya bada tabbacin za a gurfanar da shi a gaban kotu bayan kammala bincike.