✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama dan bindiga da makaman AK-47 guda 53 a Nasarawa

An gano albarusai 260 a hannun dan bindigar da ake nema ruwa a jallo.

’Yan sanda sun cafke wani matashi a lokacin da yake tsaka da safarar kayan bindigogi kirar AK-47 guda 53 a Jihar Nasarawa.

Jami’an tsaron sun kuma gano albarusan bindigogin akalla guda 260 a wurin mutumin da ya shiga hannu a ranar Asabar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta ce matashin da ta kama mai shekara 35 ya shiga hannu ne a hanyarsa ta safarar makaman zuwa garin Jos, Jihar Filato.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin Rundunar, ASP Ramhan Nansel, ya ce dubun matashin ta cika ne a Kwanar Alushi da ke Karamar Hukuamr Akwanga ta Jihar.

Binciken Aminiya ya gano matashin da aka kama kasurgumin dan fashi ne da ake nema ruwa a jallo a Jihar ta Nasarawa.

Yaranshi sun yi gaba a kan babura, a hanyarsu ta zuwa Jos, bayan tahowarsa da makaman ne ya fada hannun  jami’an tsaro.

Kakakin ’yan sandan ya ce, “An ga wani kasurgumin dan fashi da Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa take nema ruwa a jallo saboda aikata fashi da garkuwa da mutane a Alushi Junction, Karamar Hukumar Akwanga.

“Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Akwanga ya tura jami’ai nan take inda suka kama matashin mai shekara Likita 35 dauke da albarusai 260 da mazuban albarusai 53 da kuma tsabar kudi N38,500.”

Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Adesina Soyemi ya sa a gudanar da cikakken bincike sannan a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.