An kama uwa da ’yarta kan antaya wa wata mata ruwan zafi | Aminiya

An kama uwa da ’yarta kan antaya wa wata mata ruwan zafi

‘Yan sanda
‘Yan sanda
    Sagir Kano Saleh

Wata matar aure tare da ’yarta budurwa sun watsa wa wata mata ruwan zafi kan wani sa-in-sa da suka samu a Jihar Legas.

Uwa da ’yar sun yi wa matar wannan aika-aika ne da misalin karfe 12 na dare aunguwar Igbanko da ke jihar.

Dan sanda mai gabatar da kara ne ya bayyana haka, bayan an gurfanar da matar mai shekarar 48 ne tare da ’yar tata mai shekara 16 a gaban Kotun Majistare da ke zamanta yankin Badagri, Jihar Legas.

Mai gabatar da kara, ASP Clément Okuoimose, ya ce wadanda ake zargin sun watsa wa matar ruwan zafi ne a ranar 28 ga watan Mayu da ya gabata.

Bayan saurarar karar, alkalin kotun, Fadahunsi Adefioye, ya bayar da belin wadanda ake zargin a kan N100,000 kowannensu, sannan su kawo mutum biyu da za su tsaya mutu.

Daga nan kotun ta dage zamanta zuwa ranar 22 ga watan Yuni da muke ciki domin ci gaba da shari’ar.