✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala kada kuri’a a zaben Kano

Tuni dai aka kammala kidaya kuri’u a mazabu da dama, yayin da ake ci gaba da tattara sakamako a matakan mazabu da na Kananan Hukumomi

Yayin da aka kammala kada kuri’a ilahirin mazabu a zaben Kananan Hukumomin Jihar Kano, yanzu haka hankula sun fara komawa zuwa ga Hukumar Zaben Jihar Mai Zaman Kanta (KANSIEC) inda ake dakon sakamako.

Tuni dai aka kammala kidaya kuri’u a mazabu da dama, yayin da ake ci gaba da tattara sakamako a matakan mazabu da na Kananan Hukumomi kafin a sanar da sakamako na karshe.

Jam’iyyu 18 ne dai suke fafatawa a zaben, ciki har da jam’iyyar adawa ta PDP, duk kuwa da barazanar da ta yi na maka KANSIEC a gaban kuliya muddin ta kuskura ta saka ta a cikin takardar zaben.

Zaben, wanda ya fuskanci karancin fitowar masu kada kuri’a dai ya gudana lafiya a mafi yawancin sassan jihar.

Sai dai a mafi yawancin mazabun da Aminiya ta ziyarta, ta iske akasarin wakilan jam’iyyar APC ne a wuraren akwatunan zaben, yayin da wakilan sauran jam’iyyu 17 suka ki fitowa.

Kazalika, Aminiya ta kuma lura cewa a mafi yawa daga cikin unguwannin cikin birnin Kano, matasa sun rika kashe manyan tituna sakamakon takaita zirga-zirgar ababen hawa inda suka rika raba kwallo a kan su.

Galibinsu dai sun bayyana zaben a matsayin ‘bata lokaci da asarar kudade’ saboda sun ce tuni sun riga sun san wadanda za su yi nasara.

A wani labarin kuma, wani wakilin Aminiya ya sha da kyar a hannun wasu ’yan daba a mazabar Tudun Bojuwa da ke Kurnar Asabe a Karamar Hukumar Dala bayan da suka kwace masa waya.

’Yan dabar dai sun tilasta masa goge dukkanin hotuna da bidiyoyin da ya dauka kafin daga bisani su ba shi wayar tare da korar sa daga mazabar bisa zargin cewa wata jam’iyyar yake yi wa aiki.