✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama kamfanin giya a matsayin wanda ya fi kowanne biyan haraji a Kaduna

Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta karrama Kamfanin Giya na Nigerian Breweries da kyauta mafi girma a matsayin wanda ya fi biyan…

Hukumar Tattara Kudaden Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) ta karrama Kamfanin Giya na Nigerian Breweries da kyauta mafi girma a matsayin wanda ya fi biyan haraji a jihar.

Shugaban hukumar, Dakta Zaid Abubakar ne ya bayyana kamfanin a matsayin wanda ya zama zakaran gwajin dafi yayin wata walimar karramawa da aka gudanar a Kaduna ranar Juma’a.

Shugaban ya yi kira ga sauran hukumomi da kamfanoni su kwaikwayi kamfanin wajen biyan harajinsu yadda ya kamata ba tare da an tursasa musu ba.

“Makasudin bayar da wannan kyautar shine domin mu zaburar da mutane su ci gaba da biyan harajinsu domin samun ci gaba da bunkasa rayuwar al’umma.”

Da yake gabatar da kyautar ga Manajan kamfanin na Nigerian Breweries a jihar, Mista Abbay Ajayi, Babban Sakatare a Ma’aikatar Kudi ta jihar, Murtala Dabo ya yabawa kamfanin saboda ficen da ya yi.

Da yake karbar kyautar, Mista Ajayi ya ce kamfanin nasu ya biya kudaden harajin da suka kai kusan Naira biliyan 330 a cikin shekaru biyar da suka gabata ga Najeriya, wanda daga ciki jihar ta Kaduna ta amfana da kusan Naira biliyan daya da miliyan 400 tsakanin 2018 da 2020.

“Mun kuma biya Naira miliya 315 ga Hukumar Samar da Ruwan sha ta jihar daga shekarar 2016 zuwa yanzu.

“Tun bayan kafa kamfaninmu, mun zuba jarin kusan Naira biliyan 45 kuma muna shirin sake zuba jarin wata biliyan bakwai din a jihar a iya 2021 kawai,” inji shi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewaan karrama jimlar kamfanoni 23 domin karfafa gwiwarsu su ci gaba da biyan harajin a kashin kansu domin ci gaban jihar.