✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 12, wasu da dama sun bace a kauyen Katsina

Maharan sun kuma yi wa mata fyade sannan suka tafi da daruruwan dabbobi.

’Yan bindiga sun kai hari kauyen Duba da ke Karamar Hukumar Batsari a Jihar Katsina tare da kashe mutum 12, wasu kuma da dama suka ji rauni.

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu cewa kauyen, wanda ke da nisa wasu ’yan kilomitoci daga garin Batsari ya fuskanci harin ne da yammacin ranar Asabar.

Kazalika, ya ce maharan sun kuma yi wa matan garin fyade sannan suka tafi da daruruwan dabbobi.

A cewar majiyar, “Gungun maharan sun shigo garin ne da yamma sannan suka aikata ta’asar ba tare da sun fuskanci kowanne irin martani ba.

“Maganar da nake da kai yanzu haka, mun tabbatar da mutuwar mutum 12, yayin da muke ci gaba da duba dazukan da ke kusa da garin ko za mu kara samun wasu gawarwakin.

“A ’yan kwanakin nan, ’yan bindiga sun matsa mana da hari matuka, suna karkashe mutane kusan a kullum ba tare da kowanne irin tarnaki ba. Kawai karensu suke ci ba babbaka,” inji majiyar.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da faruwar harin inda ya ce sun sami rahoton kisan  mutum 12, yayin da mutun shida suka samu raunuka.

Ya kuma ce maharan har ila yau, sun kwashi kaya a shagunan cikin garin.

Ko da yake bai sanar da kama kowa ba, ya ce rundunar na ci gaba da bincike a kai.

Karamar Hukumar Batsari dai na daga cikin Kananan Hukumomin da suka fi fuskantar hare-haren ’yan bindiga a Jihar ta Katsina.

SAURARI:Abin Da Ya Sa Hukumomi Suka Kasa Shawo Kan Kwalara