✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori Ministar Harkokin Wajen Libya kan tattaunawa da Isra’ila

Ministar da aka kora ta tsere daga Libya bayan tattaunawarta da takwararta ta Isra'ila ya jawo bore a kasar.

Gwamnatin Libya ta kori Ministar Harkokin Wajen kasar, Najla al-Mangoush, kan wata ganawa da ta yi da gwamnatin Isra’ila.

Rahotanni sun ce ministar da aka kora ta tsere daga Libya bayan tattaunawarta da takwararta ta Isra’ila ta jawo bore a kasar, inda gwamnati ta sa a bincike ta.

Gwamnatin Fira Minista Abdelhamid Dbeibah da ke goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ministar ce bayan ganawarta da Isra’ila ya jawo bore a kasar, wadda ba ta aminta da Isra’ila a matsayin halastacciyar kasa ba.

A makon jiya ne Najla al-Mangoush ta tattauna da dakwararta ta Isra’ila, Eli Cohen, a birnin Rome na kasar Italiya, a matsayin wani yunkuri na daidaita alaka tsakanin kasashen Larabawa da Isra’ila.

Ganawar tata ta haifar da bore da kone-kone a sassan Libya ranar Lahadi, inda masu zanga-zanga dauke da tutocin Falasdinu suka tare hanyoyi.

Kafin zuwansa a Ofishin Jakadancin Falasdinu a ranar Litinin, Fira Minista Dbeiba ya sanar da dakatar Najla al-Mangoush da kuma ba da umarnin a bincike ta, bayan Isra’ila ta tabbatar cewa zaman ya wakana.

Majalisar Dokokin kasar da ke goyon bayan Falasdinu da Isra’ila ke wa danniya, ta bukaci a binciki ministar, inda a lokacin zaman ’yan majalisar suka sanya rawanin Faladinawa mai launin fari da baki, domin nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu.

Hukumar tsaron cikin gidan Libya ta sanar cewa dakatacciyar ministar ba ta izinin fita daga kasar ba, hasali ma an harmta mata tafiye-tafiye sai an kammala bincike.

Amma kafar yada labarai ta Anadolu da ke kasar Turkiyya ta ruwaito wasu majiyoyin tsaro a Libya na cewa bayan tataburzar, Najla ta fice daga kasar zuwa Turkiyya.

Ma’aikatar harkokin waje da Najla ke jagoranta kafin a dakatar da ita ta fitar da watta sanarwa cewa ganwarta da Cohen “wata dama ce, amma ba a hukumance aka yi ba, kuma ta fada babbar murya cewa Libya na goyon bayan Falasdinawa 100 bisa 100.”

Ma’aikatar ta zargi kuma Isra’ila da neman nuna wa duniya cewa a hukumance suka tattauna a zaman da ake ganin gwamnatin Amurka ce ta tsara.

Masu sharhi na ganin ministar ta yi tattaunawar ne a bisa ra’ayin gwamnatin adawar kasar, wadda ba ta goyon Majalisar Dinkin Duniya — sabanin matsayin gwamnatin Fira Minista Abdelhamid Dbeibah, wadda ba ta kallon Isra’ila a matsayin halastacciyar kasa.

Tun bayan hambarar da tsohon shugaban Libyan Mu’ammar Kadhafi kasar ke cikin rikici, inda aka samu gwamnatoci masu adawa da juna, a sassan kasar.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta aminta ne da wadda ke da hedikwatar a birnin Tripoli karkashin jagorancin Fira Minista Dbeiba, wanda shi kuma ya bayyana cikakkiyar goyon bayansa ga al’ummar Falasdinawa, wadanda Isra’ila ta mamaye wa kasa.