✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantar da ‘yan bindiga suka kwashi dalibai a Kaduna

Da wakilan Aminiya suka ziyarci makarantar, sun iske daruruwan dalibai na kokarin fita da kayayyakinsu.

Biyo bayan sace dalibai 39 sakamakon harin ’yan bindiga a Kwalejin Fasahar Aikin Gona dake Kaduna a daren ranar Alhamis, hukumar makarantar ta sanar da rufeta har sai abin da hali ya yi.

Akalla dalibai 180 da sojoji suka kubutar daga hannun ’yan bindigar kuma suka kai su Makarantar Horar da Sojoji ta NDA a ranar Juma’a ne ne suka koma makarantar da nufin kwashe komatsansu su koma gida a ranar Asabar.

Daya daga cikin daliban mai suna Haruna Shehu wanda ke aji biyu ya ce hukumar makarantar ce ta umarce su da su tafi gida kuma su zauna a can har sai abin da hali ya yi.

Lokacin da wakilan Aminiya suka ziyarci makarantar, sun iske daruruwan dalibai na kokarin tafiya gida dauke da kayayyakinsu.

Shugaban makarantar, Dakta Usman Mohammed Bello ya tabbatar da rufe makarantar inda ya ce an umarce su ne su rufe ta har zuwa wani lokaci a nan gaba.

“Gaskiya ne mun rufe makarantar tun jiya [Juma’a], amma wasu daga cikin dalibanmu da aka kai barikin sojoji sune suka dawo yau [Asabar] suka kwashe kayayyakinsu kafin su wuce gida. Hatta jarrabawar ma da aka tsara yi mako mai zuwa yanzu ita ma an dage sai nan gaba,” inji Dakta Bello a zantarwarsa da wakilinmu ta wayar salula.