✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantu a Zamfara bayan sace daliban Kankara

Gwamnati ta ce daukar matakin ya zama dole domin kare rayuwar dalibai

Jihar Zamfara ta rufe makarantunta a yankunan da ke iyaka da jihohin Katsina da Kaduna masu fama da matsalar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.

A sanarwar da ta fitar ranar Talata, Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce umarnin makarantu 10 ne aka rufe, a matsayin kandagarki, la’akari da yanayin tsaro.

Kwamishinan Ilimin Jihar, Dokta Ibrahim Abdullahi Gusau, ya ce: “Abin da ya faru a makwabciyarmu jiyar Katsina ya tilasta mana rufe wadannan makarantu duk da cewa saura mako guda zangon karatun da ake ciki zai kare”.

Ya ce daukar matakin ya zama dole don a dakile rashin doka da oda a da kuma tabbatar da tsaron dalibai; duk da cewa za a ci gaba da sha’anin koyo da koyarwa a sauran makarantu.

“Makarantun da [umarnin] ya shafa na wurare ne da ke kan iyakar jiharmu da makwabtanmu, Katsina da Kaduna”, inji shi.

Makarantun da aka rufen su ne:

  1. G.S.S. Tsafe (Raka boarding)
  2. G.S.S Birnin Magaji (Boarding)
  3. G.D.S.S. Nasarawa Mailayi (je-ka, ka-dawo)
  4. G.D.S.S. Gusami (je-ka, ka-dawo)
  5. G.A.S.S. Zurmi (ta kwana)
  6. G.D.S.S. Gurbin Bore (Je-ka, ka dawo)
  7. G.G.S.S. Moriki (ta kwana)
  8. Science Secondary School, Shinkafi (ta kwana)
  9. Science Secondary School, Dansadau (ta kwana)
  10. Science Secondary School Bakkuyaum (ta kwana)