✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace Shugaban wata makarantar Gwamnatin Tarayya da ke Kaduna

Sun kuma sace wata budurwa bayan kashe mutum daya

’Yan bindiga sun kashe mutum daya tare da yin awon gaba da shugaban Makarantar Kididdiga ta Gwamnatin Tarayya (Federal School of Statistic) da ke Manchok, hedkwatar karamar hukumar Kaura ta jihar Kaduna.

Lamarin, kamar yadda wani mazaunin yankin ya shaida wa Amimiya, ya faru ne da misalin karfe 9:00 na daren Talata.

Ya ce maharan sun shigo yankin suna harbe-harbe, inda suka kashe mutum daya tare da awon gaba da wata burdurwa da kuma shugaban Makarantar.

Wannan harin na zuwa ne mako biyu bayan kashe wasu jami’an raba gidajen sauro mutum biyu a hanyar Zankan zuwa Zangan dake karamar hukumar ta Kaura.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu wata sanarwa daga gwamantin jihar Kaduna a kan farmakin.

Kazalika, Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige bai amsa kiran wayar wakilinmu ba yayin hada wannan rahoton.