✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za mu kori duk wani azzalumin alkalin kotun Musulunci —Gwamnatin Borno

Sabbin alkalan kotunan Shari'ar Musulunci 21 sun karbi rantsuwar fara iki a Jihar Borno.

Gwamnatin Jihar Borno ta ce za ta kori duk wani alkalin kotun Musulunci da aka samu da hannu a almundahana ko zalinci.

Babban Alkalin Jihar Borno, Mai Shari’a Kashim Zannah, ne ya bayyana haka a lokacin da yake rantsar da Sabbin alkalan kotunan Shari’ar Musulunci 21 a ranar Talata.

Mai Shari’a Kashim Zannah, ya shaida musu cewa, “Za mu hukunta duk wanda muka kama ta hanyar tozarci da kora daga aiki, ba wai mu yi mishi sauyin wurin aiki ko rage mukami ba.”

Don haka ya bukace su da su kasance masu adalci wajen yin shari’a, kamar yadda suka rantse za su yi.

Ya kara da cewa , “Kowannenku ya samu wannan mukamin ne bisa cancanta babu alfarma, don haka babu dalilin ku yi tantamar maganarmu cewa ba za mu lamunci kowane irin almundahana ba.”

“Ba mu da wani zabi da ya fi mu nada ku a wannan matsayi tunda kowannenku ya cika sharuddan da aka gindaya.

“Kowannenku yana sane da ka’idar da aka sanya a wuraren da aka tura ku bayan samuwar zaman lafiya kuma ya amince.

“Saboda haka da zarar gwamnati ta samar da kayan aiki za ku wuce wurin aikinku ba tare da bata lokaci ba.

“Muna kira ga hukumomin yankunan da su ba ku damar mallakar filayen noma domin bunkasa samar da abinci da kudaden shiga ta halastacciyar hanya.”

Tun da farko, Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya ( NBA), Reshen Jihar Borno, Barista Abba Malam Ummate, ya yaba wa gwamnatin jihar bisa manyan ayyukan da ta gudanar a bangaren shari’a ta kuma kammala su a kan kari.