✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An saka kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a kasuwa

Kamfanin FSG wanda ya mallaki kungiyar kwallon kafa ta Liverpool a kasuwa

Kamfanin FSG wanda ya mallaki kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da ke Ingila, ya sanya kungiyar a kasuwa.

Rahotanni sun ce kamfanin ya yanke shawarar sayar da kungiyar ne ’yan watanni bayan an sayar da takwararta ta Chelsea a kan Yuro biliyan 4.25.

FSG, wanda kamfanin kasar Amurka ne dai ya sayi Liverpool ne daga George Gillett da Tom Hicks a watan Oktoban 2010.

Ya zuwa watan Mayun 2022, mujallar Forbes ta ce darajar Liverpool ta kai Dalar Amurka biliyan 4.45, kwatankwacin Yuro biliyan 4.25.

To sai dai la’akari da yadda aka sayar da Chelsea ga mamallakin kamfanin LA Dodgers, Todd Boehly a kan Yuro biliyan 4.25 a farkon wannan shekarar, akwai yiwuwar su ma su bukaci a sayi ta su a kwatankwacin wannan farashin.

A baya dai, FSG ya ce a shirye yake ya amince da masu tayin sayen hannun jari a kungiyar, kuma a shirye yake ya amince da hakan matukar an cika sharuddan da ya gindaya.