✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mata ’yan majalisa na so a nada mace Ministar Tsaron Najeriya

Sun ce matukar aka nada mace a natsayin, za a ga aiki da cikawa

Kungiyar Mata Mambobin Majalisar Dokoki ta Kasa sun yi kira da a nada mace a matsayin Ministar tsaro a Najeriya.

Shugabar kungiyar, Hon. Taiwo Oluga, ce ta yi kiran lokacin da take jawabi ga manema labarai a Abuja ranar Litinin.

A cewarta, matukar aka nada mace a kan mukamin, matsalar tsaron da ke addabar Najeriya za ta zama tarihi.

Ta ce, “A karon farko a tarihi, ya kamata a nada mace a wannan matsayin idan ana so a ga aiki da cikawa; za a ga sakamako mai kyau na ingantuwar yanayin tsaro.

’Yar majalisar ta ce abin takaici ne ganin cewa duk da fafutukar da kungiyoyin mata ke yi na kara yawan mata a harkokin siyasar kasar, har yanzu ba a sami wani ci gaba na ku-zo-ku-gani ba.

“La’akari da yawan matan da yanzu haka suke takarar mukaman siyasa daban-daban a zaben 2023 da ke tafe, za mu iya cewa abin damuwa ne saboda akwai yiwuwar yawan mata ya ragu a majalisa ta gaba.

“Kafin zabukan fid-da gwanin da aka kammala, Najeriya na cikin kasashen da ke da karancin wakilcin mata a majalisu, inda kaso 6.2 cikin 100 na mata ne kawai a cikinsu. Wannan abin damuwa ne matuka,” inji ta.

Taiwo Oluga ta kuma ce a wasu jihohin irin su Sakkwato da Kano da Taraba da Yobe da Zamfara, babu mace ko guda daya da aka tsayar takarar kowacce kujera a zabukan na 2023.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an shirya taron ne tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Asusun Tallafa wa Matan Najeriya. (NAN)