✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kai wa ofishin ’yan sanda hari a Imo

An yi garkuwa da jami'in dan sanda; Hari na uku cikin kwana uku a ofisohin ’yan sanda a Jihar

’Yan bindiga sun sake kai sabon hari a wani ofishin ’yan sanda a Jihar Imo, inda suka yi awon gaba da jami’in dan sanda suka kuma saki tsararru.

Da misalin karfe 1 na dare kafin wayewar garin Alhamis ne ’yan bindigar suka kai farmaki a kan Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Mbieri, Karamar Hukumar Mbaitoli ta Jihar.

Kwana na hudu cikin kasa mako daya ke nen da ’yan bindiga suka hare-hare a kan cibiyoyin tsaro a Jihar, inda daga watan Fabarairu zuwa yanzu aka kai hari a kan Manyan Ofishoshin ’Yan Sanda guda shida.

A rnaar Litinin an wayi gari da labarin harin ’yan bindiga da ake zargin ’yan kungiyar IPOB ne suka kai hari a Hedikwatar ’Yan Sandan Jihar Imo, suka cinna masa wuta, suka kona motoci suka kuma saki tsararru.

Daga can suka kai hari inda suka balla Gidan Yarin Owerri, suka saki fursunoni kusan 2,000.

Bayan nan a sai da suka kar kai hari, suka saki tsararru, a ranar Talata a Jihar a yayin da Sufeto Janar na ’Yan sanda yake jihar domin gane wa idonsa abin da ya faru.