✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin Tambuwal da haddasa rikici a jam’iyyar PDP

Kowa ya san jihar Kano ita ce cibiya kuma jigon siyasar Arewacin Najeriya.

Wani jigo na jam’iyyar PDP a Jihar Kaduna, Alhaji Adamu Musa Lere, ya yi zargin cewa Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, na neman haddasa rikici a jam’iyyar don cimma muradinsa na tsayawa takarar Shugaban Kasa a zaben 2023. 

Wannan na zuwa ne daidai lokacin da jam’iyyar ke shirin gudanar da zaben shugabanninta na shiyyar Arewa maso Yamma, wanda aka cimma matsaya a taron da ta gudanar na masu ruwa da tsaki.

Da yake tattauna da Aminiya ta wayar salula, Lere ya ce “Wannan wani yunkuri ne da Gwamna Tambuwal ke yi don kawo rudani da rikici a tafiyar jam’iyyar PDP a jihar Kano da ma shiyyar Arewa maso Yamma baki daya.

“Kowa ya san jihar Kano ita ce cibiya kuma jigon siyasar Arewacin Najeriya wacce take da tarin kuri’u, don haka wannan ka iya jefa jam’iyyar PDP cikin wani hali duba da karatowar zaben 2023,” a cewar Lere.

Lere ya zargi Gwamna Tambuwal da yin watsi da tsarin da masu ruwa da tsaki na jami’iyyar suka gabatar a taron da suka gudanar ranar 1 ga watan Maris na 2021.

Kazalika, Lere ya yi zargin cewa Gwamna Tambuwal na shirin siya wa wani makusancinsa kuma jigo na jam’iyyar PDP a Jihar Kano, tikitin takarar Mataimakin Shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Yamma.

Lere ya bukaci uwar jam’iyyar PDP ta kasa da ta shiga cikin lamarin don samar da daidaito tare da kaucewa samun baraka a cikin jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ware ranar Asabar 10 ga Afrilun, 2021 a matsayin ranar da gudanar da taron a Jihar Kaduna.

Sai dai hadimin Gwamnan kan kafafen yada labarai, Muhammad Bello, ya musanta wannan zargi da wani tsagi na jam’iyyar PDP suka yi.

A zantawarsa da Aminiya, Malam Bello ya ce a kowace jam’iyya duk wanda aka yi wa ba daidai ba, yana da damar fadin albarkacin bakinsa kuma ire-ire wannan babatu sukan fito ne daga bangaren wadanda ke neman huce takaicinsu.

“Gwamna Tambuwal na kokarin ya kawo zaman lafiya ne jam’iyyar tare da sanya kowa a cikin tafiyarsa kasancewarsa Shugaban Gwamnonin PDP.”

“Da ya ke siyasa ake yi kowa na da ‘yancin fadar albakacin bakinsa, amma maganar Tambuwal na neman haddasa fitina a PDP ba gaskiya bane,” a cewar Bello.

Kazalika, ya ce Tambuwal ba shi da wani buri face dinke duk wata baraka da ke neman tasowa a jam’iyyar musamman daga shiyyar Arewa maso Yamma.