✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An soma bincike kan mutuwar kifaye a Jamus

Mahukunta sun fitar da sanarwar gargadin bala’in muhalli a yankin.

Mahukunta a Jamus sun soma bincike don gano yadda aka samu yawaitar matattun kifaye a kogin Oder ta ya ratsa ta cikin kasar da kuma makwabciyarta Poland.

Wannan lamari dai ya haifar da gargadin bala’in muhalli yayin da aka bukaci mazauna yankin da su kaurace wa ruwan.

Tuni dai aka soma bincike don gano sinadarin da ka iya haddasa mutuwar kifayen, wanda rahotannin farko suka nuna alamun yawan ruwan sinadarin dalma.

Sai dai wani kashi na sakamakon farko da aka fitar a Yammacin ranar Juma’a, ya nuna yawan gishirin da ba a saba gani ba.

Matattun kifayen da ke shawagi a saman ruwa a garin Schwedt da ke gabashin Jamus, ana kyautata zaton sun kwaroro ne daga magudanar ruwan Poland, inda aka samu rahotannin farko na mutuwar kifaye da yawa tun ranar 28 ga watan Yuli.