✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

El-Rufai ya haramta amfani da babura a Kaduna

Daga ranar Alhamis, 30 ga Satumba, 2021 za a rufe layukan sadarwa a wasu sassan Jihar.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da toshe layukan sadarwa a wasu kananan hukumomin jihar tare da haramta amfani da babura masu kafa biyu gaba daya a fadin jihar.

Kwamihinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, ya sanar da cewa matakan za su fara aiki ne daga ranar Alhamis, 30 ga Satumba, 2021.

Aruwan ya sanar wa manema labarai a ranar Laraba cewa, “Ina sanar da ku a hukumance cewa za a fara aiwatar matakan tsaro da aka dauka domin ba wa hukumomin tsaro goyon baya a wasu sassan jihar nan.

“Hukumomin Gwamnatin Tarayya sun sanar da Gwamnatin Jihar Kaduna cewa an fara bin matakan aiwatar da toshe layukan sadarwa a sassan jihar domin shawon kan matsalar tsaro da jihar da makwabtanta a yankin Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta Tsakiya.”

Aruwan ya sanar cewa “Gwamnatin Jiha Kaduna ta sha yin zama da hukumomin tsaro inda suka yi ittifakin daukar matakan murkushe ’yan bindiga a maboyarsu.

“An shawarci gwamnatin jihar ta dauki matakan da yanzu suke taimaka wa ayyukan hukumomomin tsaron.

“Daga ranar Alhamis, 30 ga Satumba wadannan matakan za su fara aiki:

“Haramta amfani da baburan haya da na kashin kai na tsawon wata uku a karon farko; haka ma mallaka ko daukar muggan makamai.

“Babura masu kafa uku kuma an takaita ayyukansu zuwa karfe 6 na safe zuwa bakwai na yamma, sannan wajibi ne su cire labulensu.

“Dole ne duk motocin haya su kasance da fentin baki da ruwan kwai daga yanzu zuwa kwana 30 masu zuwa.

“An haramta sayar da fetur a cikin jarkoki da sauran mazubai a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kachi, Kagarko da kuam Kajuru.”

Ya kara da cewa sauran matakan da gwamnatin jihar ta dauka a baya na magance ayyukan bata-garin har yanzu suna nan sun aiki.

Matakan sun hada da haramcin sare itatuwa a Kanana Hukumoin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun, Kachia, Kagarko da kuma Kajuru.

“Akwai kuma haramci a kan fataucin gawayi da dabbobi da zuwa jihar da Kaduna ko daga jihar zuwa wasu jihohin.

“An kuma rufe kasuwannin mako-mako a kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Chikun, Igabi, Kajuru da Kasuwa Kawo da ke Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa.