✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsaurara tsaro a Kano bayan rahoton kai hari hedikwatar ‘yan sanda

An yada rahoton cewa wasu mahara sun yi harbe-harbe a hedikwatar 'yan sanda ta Zone 1.

Jami’an tsaro sun yi shirin ko ta kwana a wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano sakamakon rahoton harbe-harbe da aka ce ‘yan bindiga sun yi a hedikwatar ‘yan sanda ta Zone 1 da ke jihar.

Ko da yake rundunar ‘yan sandan ta musanta cewa an yi harbe-harbe a hedikwatar da ke kan titin tsohuwar Jami’ar Bayero (BUK), amma an lura da yammacin ranar Juma’a, an rufe hannun titin da hedikwatar ‘yan sandan take, inda masu ababen hawa ke aron hannu a babban titin mai hannu biyu.

Kazalika, titin shiga gidan gwamnatin jihar ma an toshe shi, lamarin da ya sa dole masu amfani hanyar ke bin wasu hanyoyin na daban.

Haka kuma, wasu wurare kamar barikin ‘yan sanda da ke kan titin Maiduguri a unguwar Hotoro shi ma ya kasance a rufe.

Zagayen da Aminiya ta yi ta lura cewa, an kuma jibge jami’an tsaro da dama tare da toshe hanyoyin wasu wurare a birnin na Dabo.

Wani babban jami’in tsaro a jihar da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa, manufar rufe hanyoyin da kuma kara jami’an tsaro a wurare daban-daban na da nasaba da harin da aka kai da kuma bayanan sirri da aka samu.

Majiyar ta ce rundunar hadin gwiwar jami’an tsaro a jihar na aiki ne kan bayanan sirrin da ke nuna cewa lamarin ba zai rasa nasaba da ‘yan ta’addan Boko Haram da ake zargi ba.

A Juma’ar nan ce wani rahoto ya bayyana cewa wasu ‘yan bindiga a motoci uku sun yi harbe-harbe da misalin karfe 12:30 na rana a hedikwatar ‘yan sandan ta Zone 1, inda daga bisani suka tsere daga wurin, lamarin da majiyar ‘yan sandan ta musanta cewa babu wani hari ko yunkurin kai hari da aka kai musu.

Wasu mutanen da ke kan hanyar sun ce sun ji karar harbe-harbe, amma babu wanda zai iya tabbatar da cewa ga abin da aka harba, amma an tabbatar da cewa an gudanar da Sallar Juma’a a Masallacin Juma’a da ke cikin hedikwatar da misalin karfe 1 na rana.

Kakakin ‘yan sandan hedikwatar ta Zone 1, ya yi alkawarin cewa nan gaba kadan zai yi karin haske game da lamarin bayan da wakilinmu ya tuntube shi.