✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnan Sakkwato ya tube rawanin hakimai 15

Gwamnatin Sakkwato ta sallami hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauran laifuka. An sallami hakimai 9 daga mukamansu bisa…

Gwamnatin Sakkwato ta sallami hakimai 15 bisa zargin su da taimakawa rashin tsaro, satar filaye da sauran laifuka.

An sallami hakimai 9 daga mukamansu bisa zargin su da rashin biyayya da taimakon rashin tsaro da satar filaye da kuma karkatar da dukiyar jama’a da rashin da’a.

Wadanda aka sallama su hada da hakiman Uguwar Lalle, Yabo, Wamakko, Tulluwa, llela, Dogon Daji, Kebbe, Alkammu, da kuma Hakimin Gyawa.

Gwamnatin jihar ta kuma sauke wasu hakimai shida da tsohuwar gwamnatin jihar ta nada.

Abubakar Bawa, Sakataren yada labarai na Gwamna Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa an sauke hakiman shida ne saboda yadda aka nada su bisa ga ka’ida da kuma kin amincewa da mutanensu suka yi.

Su hada da hakimin Marafan Tangaza, Sarkin Gabas Kalambaina, Bunun Gongono, Sarkin Kudun ’Yar Tsakkuwa, da kuma  Sarkin Tambuwal da Sarkin Yamman Torankavwa.

Bawa ya kara da cewa “An yaba da kararrakin da suka shafi Hakiman Isa, Kuchi, Kilgori da Gagi don ci gaba da bincike.”

Sai dai Sarkin Yakin Binji, babban mai ba da shawara a Majalisar Suktanate an mayar da shi Nabunkari yayin da Hakimin Sabon Birni ya kai Gatawa.

Bawa ya lura cewa, an bar wasu hakimai bakwai a kan kujerunsu da suka hada da Alhaji Aliyu Abubakar III (Shugaban Sokoto); Alhaji Ibrahim Dauki Maccido (Barayar Zaki); Abubakar Salame (Sarkin Arewan Salame) da Aminu Bello (Sarkin Yamman Balle).

Sauran su ne Mahmoud Yabo (Sarkin Gabas Dandin Mahe); Muntari Tukur Ambarura (Sarkin Gabas Ambarura) da Malam Isa Rarah (Sarkin Gabas Rarah).

Hakazalika, Hakiman Tsaki da Asare suma an rike su yayin da aka mayar da Abdulkadir Mujeli a matsayin Sarkin Rafin Gumbi.