✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An tsinci gawar attajirin Rasha a otel din Indiya

Pavel Antov ya yi kaurin suna wajen caccakar kasar Ukraine a halin rayuwarsa.

An tsinci gawar hamshakin attajirin nan na kasar Rasha, Pavel Antov, a Indiya.

An gano gawar Pavel ne a wani otel da ke Jihar Odisha a kasar ta Indiya a ranar Asabar.

Rahotanni sun ce, wannan na zuwa ne kwana biyu bayan gano gawar wani dan jam’iyyar su Pavel din a wannan otel din da shi ma aka tsinci tasa gawar.

Gwamnatin kasar Indiya ta ce ta fara bincike kan batun domin bankado hakikanin abin da ya faru.

A shekarar 2019 mujallar Forbes ta ayyana marigayi Pavel Antov a matsayin wanda ya fi kowa arziki a tsakanin ’yan siyasar Rasha.

Hukumomi sun ce a lokacin da yake raye, Pavel ya yi kaurin suna wajen caccakar Ukraine dangane da yakin da take gwabzawa da Rasha.