✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar jaririya a gefen hanya a Hadejia

An tsinci gawar jaririyar ce ranar Lahadi a rukunin gidaje na Kandahar.

An tsinci gawar wata jaririya yashe a gefen hanya a Karamar Hukumar Hadejia ta Jihar Jigawa.

Mai magana da yawun Hukumar Tsaro ta Sibil Difens, CSC Adamu Shehu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Dutse, babban birnin jihar.

Mazauna sun ce an tsinci gawar jaririyar ce ranar Lahadi a rukunin gidaje na Kandahar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito jami’an sun mika gawar jaririya zuwa Babban Asibitin Hadejia inda wani likita ya tabbatar ta riga mu gidan gaskiya.

Adamu ya ce daga nan an mika gawar jaririyar a hannun mai unguwar yankin mai suna Malam Sani Afenza, wadda aka yi wa sutura kuma aka kaita makwacin karshe.

Mai magana da yawun ya shaida wa maname labarai cewa, za su ci gaba da gudanar da bincike a kan wannan lamari kuma duk wanda aka samu da hannu a aika-aikar zai girbi abin da ya shuka.