✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar wata mata a dakin otal a Legas

'Yan sanda sun ce sun tarar da gawar kumfa na fita ta hancinta, kuma wanda aka gansu tare a masaukin ya yi batan dabo.

An tsincin gawar wata mata mai suna Muinat a dakin wani otal da ke yankin Ikorodu a Jihar Legas.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai Najeriya (NAN) cewa, a ranar Asabar aka gano gawar.

Jami’in ya ce bayanan da suka tattara sun nuna, matar ta zo masaukin bakin ne tare da wani mai suna Alfa Sule a kan babur ranar Juma’a.

Ya ce Alfa Sule ne ya kama masaukin inda suka kasance tare da marigayiyar.

Benjamin ya kara da cewa, an gano gawar matar ce ranar Asabar da safe a lokacin da Manajan otal din ke zagayawa yana duba dakuna.

A cewarsa, an gano gawar ne alhali ba a san inda wanda suka kasance tare yake ba.

“Babu wata alamar cutarwa a jikin gawar, sannan ba a san inda Alfa Sule ya shiga ba, ya tafi ya bar babur dinsa.

“Bayan da ’yan sanda suka isa wurin, an ga kumfa na fita daga hancin gawar,” inji Hundeyin.

Jami’in ya ce za su ci gaba da zurfafa bincike har sai sun gano gaskiyar abin da ya faru.

(NAN)