✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yake wa matashi hukuncin share kotu na mako 2

An zargi matashin da tserewa da wayar da aka ba shi aro.

Wata kotun Majistare a Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin share kotun na tsawon mako biyu, saboda zargin sa da aikata cuta.

Kotun karkashin Mai Shari’a Mustapha Sa’ad-Datti, ta tuhumi matashin da laifuka guda biyu, wanda suka saba da sashe na 322 na kundin laifuka.

Tun da farko, lauya mai shigar da kara, Asma’u Ado, ta shaida wa kotun cewa mai shigar da kara, Bashir Suleiman, ya shigar da kara a sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID), a ranar 9 ga Maris, 2021.

Ta kara da cewa wanda ake zargin, ya roki wani da ya ba shi aron waya kirar Infinix S5, wanda kudinta ya kai N55,000, don ya kira dan uwansa.

Bayan ba shi wayar, sai nan take ya tsere da ita.

Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi a gaban kotun.

Hakan ne ya sa aka yanke masa hukuncin share kotun na tsawon mako biyu.