✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi fashi a kusa da Fadar Shugaban Kasa

’Yan fashi sun kai farmaki a gidan Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa.

’Yan fashi sun nemi kutsawa cikin gidan Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

An yi yunkurin yin fashi a gidan wanda ke daura da Fadar Shugaban Kasa, mai cike da tsauraran matakan tsaro ne a safiyar Litinin.

Wasu rahotanni sun ce ’yan fashin sun fasa gidan na Gambari da kuma gidan gidan wani Jami’in Gudanarwar Fadar Shugaban Kasa —duk masu makwabtaka da Fadar Shugaban Kasa— inda suka yi awon gaba da kudade da wasu kadarori.

Hakan ta sa wasu ke ganin lamarin rashin tsaro a kasar na tunkarar masu fada a ji, baya ga yadda ’yan bindiga suka addabi sauran ’yan kasa.

Amma kakakin Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya ce,  “Farfesa Ibrahim Gambari ya tabbatar cewa an yi yunkurin balla gidansa da misalin karfe 3:00 na asuba, amma ba a samu nasara ba.

“Gambari wanda gidan nasa ke layin da ke kusa da Fadar Shugaban Kasa ya tabbatar cewa babu abin damuwa game da yunkurin fashin.”

Tun bayan nada shi Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Gambari ya zabi ya koma da zama Fadar Shugaban Kasa, domin kasancewa kusa da maigidan nasa.