✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukuma a jihar Kogi

An sace shi ne a kusa da Ochadamu a karamar hukumar Ofu da ke jihar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidansa.

A ranar juma’a ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da tsohon shugaban karamar hukumar Olamaboro ta jihar Kogi, Barista Isaac Emmanuel Ekpa.

An sace shi ne a kusa da Ochadamu a karamar hukumar Ofu da ke jihar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa gidansa.

Wata majiya dake ta kusanci da wanda aka yi garkuwa da shi, ta bayyana cewa Ekpa na shirye-shiryen bikin binne mahaifiyarsa ne yayin da abin ya faru.

Da farko, masu garkuwar sun bukaci iyalansa da su ba da naira miliyan 25 kudin fansa, amma bayan daukar lokaci ana tattaunawa sun aminta a kan za su karbi miliyan 1.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kogi, Williams Ayah ya tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu inda ya ce tawagar sintiri da ke yankin Ofu sun gano mota da aka ajiye a kan hanyar yankin Ochadamu.

Ya ce a yayin da suke bincike, sun gano wani katin shaida wanda aka yar a cikin motar mai dauke da sunan Emmanuel Isaac Ekpa, wanda alamu na nuna an yar da shi ne bayan yin garkuwa da shi.

Ya ce kwamishanan ‘yan sanda, Mista Edeh ya umarci jami’an rundunar da su kara himma don farautar ‘yan bindigar tare da bin sawunsu, don a kubutar da wanda aka kama daga hannunsu.